EFCC Zata Gurfanar Da Murja Kunya A Gaban Kotu
Jami’an EFCC na Jihar kano, sun kame shahararriyar ‘yar Tiktok din nan, Murja Ibrahim Kunya, saboda zargin Cin mutuncin Naira.
A takaice dai , An kama Kunya ne saboda zargin watsa Kudadan Naira don nishadi yayin zaman ta a Otal din Tahir dake garin Kano.
Jami’an Efcc sunyi amfani da kwarewa wajan kama ita Murja Lokacin Da taki ta baiyana bayan bada belin ta da akayi Watan da ya gabata.
Da farko dai an kama ta ne a watan Janairu 2025 bisa Zargin saba dokokin babban bankin Najeriya CBN, Dokar wacce ta hana Cin mutuncin naira.
An ba da ita beli na gudanarwa kafin a gabatar da ita a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano. Amma Lokacin Da Ya kamata ta dawo Don Gabatar da Ita gaban kotu Sai taki dawowa Saboda haka aka bazama Neman ta.
Duk da haka, bayan makonnin da aka dauka ana gudanar da bincike Mai zurfi da kulawa, Hukumar ya EFCC tayi nasarar kame shahararriyar ‘yar Tiktok din inda a yanzu take a cikin komar su.
Hukumar ta EFFC ta sake tsare dokokinta don aiwatar da dokokin da ke kare mutuncin kudin Najeriya da kuma yin gargadi kan ayyukan Cin zarafi ko mutuncin kudin Najeriya .
Post Comment