Alkalin Alkalai Ta Kasa Ta Sake Mika Shari’ar Nnamdi Kanu Ga Sabon Alkali

 


Babban Alkali Na Babbar Kotun Tarayyar A cikin Abuja, Mai Shari’a John Tsoho, ya sake Mai da batun shari’ar shugaban mutanen Biafra, Nnamdi Kanu, ga wani alkali.

An bayyana wannan ci gaban ne a cikin Wata sanarwa dake dauke da sa hannun lauyan Dake jagorantar Shari’ar ta Kanu, Aloy Ejimakor, ranar Asabar a Abuja.

Idan dai Zaku Iya tunawa Kanu ya nemi a dauke Shari’ar daga wurin Mai Shari’a Binta Nyako, Wanda Gwamnatin Tarayya ke tuhumar shi Kanu da ta’addanci.

Yayinda Cikin adalcin shari’a Mai Shari’a Nyako ta tsame kanta Daga fitina ta kuma canja wannan Shari’ar zuwa wurin Babbar Alkalin Alkalai Ta Kasa don sake ci gaba da ita.

A ranar 20 ga Fabrairu, Kanu, ta hanyar lauyoyinsa na shari’a, ya rubuta wa Cif Joji ta Najeriya, Mai shari’a Kekere-Ekun, Kan ta canja masa Wata kotun da za tayi Shari’ar Yayin da Kuma aka amince da Hakan.

Post Comment