An Ga Watan Ramadan A Najeriya
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da cewa an ga watan Ramadana a Najeriya.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne, a yayin wani taron manema labarai a fadarsa dake Sokoto, inda ya tabbatar da gobe asabar a matsayin 1 ga watan Ramadan na Shekarar 1446 Bayan Hijira.
A cewar Sarkin “Mun sami labarin ganin watan Ramadana a Wannan rana ta Juma’a, kuma mun tantance mun kuma amince da Batun ganin watan, don haka gobe ne 1 ga watan Ramadana”.
A ƙarshe yayi fatan Allah yasa ayi ibada karɓaɓɓiya
Post Comment