‘Yan Fansho A kasar Nijar Zasu Maka Wasu Bankuna A Kotu

‘Yan Fansho a Jamhuriyar Nijar sun yi barazanar maka wasu Bankuna a Kotu, a sakamakon rashin biyansu Alawus Alawus din su.

Sun yi barazanar daukar wannan mataki ne biyo bayan yadda bankunan suke musu wasa da hankali duk da gwamnatin kasar ta zuba kudaden domin su raba musu.

Da ake zantawa da su a jihar Damagaram, wasu daga cikin ‘yan Fanshon sun ce ya zamar musu wajibi su dauki wannan mataki, duba da yadda Rijiya ta bada Ruwa amma kuma Guga yake neman hana wa.

A cewar su, “Mun sami sakon karta kwana (sms) dake nuna gwamnatin kasarmu ta zuba kudin a cikin bankunan, amma sai yawo suke mana da hankali wajen bamu kudin da yake hakkin mu ne”.

“Akalla sau Uku muke zuwa a kowacce rana domin karbar kudaden namu, amma kullum jiya iyau domin kuwa sun gaza ba mu kudaden namu, wanda kuma babu wata gamsashshiyar magana ta kwantar da hankali ko kuma ban hakuri”

Adan haka ne suka ce ya zaman musu wajibi su maka Bankunan a kotu, domin ta tursasa su wajen basu hakkin su tunda dai gumin su ne ba kyauta zasu basu ba.

Post Comment