Rikicin PDP Ya Karu Yayin Da Aka Dakatar Da Atiku Da Wike Da Makinde Da Karin Wasu Mutane
Isaac Fayose, dan uwa ga tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Wannan sanarwar dai na zuwa ne a wani sabon rikici da ya barke a jam’iyyar, wanda ya haifar da bangarori biyu. Isaac Fayose ya kuma sanar da dakatar da wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023 Atiku Abubakar, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, tsohon gwamna Ayo Fayose, gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, da sauran mambobin kungiyar G5 masu fada aji.
Wannan furuci da Fayose ya yi ya biyo bayan rikicin da ya barke a jam’iyyar a baya-bayan nan, inda aka dakatar da Ambasada Illiya Damagum a matsayin shugaban riko na kasa. Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa (NWC) ya yi gaggawar maye gurbinsa da Alhaji Yayari Ahmed Mohammed, bisa ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar na 2017 da aka yi wa kwaskwarima. NWC, a cikin sadarwar ta, ta bukaci shugabannin jam’iyyar, masu ruwa da tsaki, da ‘yan uwa da su maida hankali yayin da suke shirye-shiryen babban taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC), wanda aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga Oktoba, 2024.
Post Comment