Ambaliyar ruwa: Dantata ya ziyarci Maiduguri, ya bayar da tallafin N1.5bn ga wadanda abin ya shafa
Shahararren dan kasuwa kuma dattijon jihar Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan 1.5 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.
Dantata ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya jagoranci tawagar daga Kano zuwa gidan gwamnatin Borno dake Maiduguri a ranar Talata.
Dattijon dan shekaru 96 a duniya ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Gwamna Babagana Zulum da gwamnati da kuma al’ummar jihar musamman wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon ambaliyar ruwa.
Post Comment