Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Maiduguri domin jajantawa al’ummar jihar Borno kan iftila’in ambaliyar da ya afkwa wa birnin.

Ziyarar tasa na zuwa ne kwanaki shida bayan mummunar ambaliyar da birnin ya fuskanta wanda rabon a ga haka tun bayan shekara 30 da suka wuce.

Ɓallewar madatsar ruwa ta Alau da ke wajen birnin ce ta haifar da mummunar matsalar.

Ambaliyar ta rutsa da mutum 37 a cewar hukumar ba da agaji ta ƙasa Nema.

Zuwa yanzu gwamnatin jihar ta ce ta yi sanadiyar ɗaiɗaita mutane sama da miliyan ɗaya.

Post Comment